2 Corinthians 2

1Don haka na yanke shawara daga bangarena, ba zan sake zuwa wurin ku cikin yanayi mai tsanani ba. 2Idan na bata maku rai, wa zai karfafa ni, in ba shi wanda na bata wa rai ba?

3Na rubuto maku kamar yadda na yi domin idan na zo gareku kada in sami bacin rai a wurin wadanda ya kamata su faranta mani rai. Ina da gabagadi game da dukan ku, cewa farincikin da nake da shi, shine kuke da shi duka. 4Domin kuwa na rubuto maku cikin kunci da bacin rai da kuma hawaye mai yawa. Ba zan so in sake bata maku rai ba. Maimakon haka, na so ku san zurfin kaunar da nake da ita domin ku.

5Idan wani ya kawo sanadin bacin rai, ba ni kadai ya kawo wa wannan abin ba, amma ta wani fannin- domin kada a tsananta- har a gare ku duka. 6Hukuncin nan da galibinku kuka yi wa mutumin nan ya isa. 7Don haka, yanzu a maimakon hukunci, ku gafarta masa, ku kuma ta’azantar da shi. Ku yi haka domin kada bakinciki mai yawa ya danne shi.

8Don haka ina karfafa ku da ku nuna irin kaunar da kuke yi masa a fili. 9Wannan shine dalilin da ya sa na rubuto maku, domin in gwada ku, ko kuna biyayya cikin komai.

10Duk mutumin da kuka gafarta wa, ni ma na gafarta masa. Abin da na gafarta-idan na gafarta wani abu-an gafarta ne domin ku a gaban Almasihu. 11Wannan ya zama haka ne domin kada shaidan ya yaudare mu. Don ba mu jahilci irin makircinsa ba.

12Na samu budaddiyar kofa daga wurin Ubangiji yayin da nazo birnin Tarwasa, in yi wa’azin bisharar Almasihu a can. 13Duk da haka, raina bai kwanta ba, domin ban ga dan’uwana Titus a can ba. Sai na bar su a can, na dawo Makidoniya.

14Amma godiya ta tabbata ga Allah, wanda cikin Almasihu yake kai mu ga nasara a koyaushe. Ta wurin mu ya baza kamshi mai dadi na saninsa ko’ina. 15Gama mu, kamshi ne mai dadi na Almasihu ga Allah, a tsakanin wadanda ake ceton su, da kuma tsakanin wadanda suke hallaka.

16Ga mutanen da suke hallaka, kamshi ne daga mutuwa zuwa mutuwa. Ga wadanda suke samun ceto kuma kamshi ne daga rai zuwa rai. Wanene ya cancanci wadannan abubuwan? Gama mu ba kamar sauran mutane muke ba, masu sayar da maganar Allah domin samun riba. Maimakon haka, da tsarkakkiyar manufa, muke magana cikin Almasihu, kamar yadda Allah ya aiko mu, a gaban Allah.

17

Copyright information for HauULB